Wasanni-Kwallon kafa

'Yan wasan Manchester United sun kware wajen yaudara - Mourinho

Jose Mourinho, kocin Tottenham.
Jose Mourinho, kocin Tottenham. REUTERS/Andrew Yates

Kocin Tottenham, kuma tsohon kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce ‘yan wasan tsohuwar kungiyar da ya horar suna da dabara wajen amaja da kuma kirkiro raunin da sam babu shi.

Talla

Mourinho yana wannan bayani ne bayan rashin nasarar da kungiyar sa ta yi a hannun Manchester United 2-1 a daren Laraba.

Kocin ya shiga a Tottenham da kafar dama, inda ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci kungiyar, amma sai aka dama mai lissafi a filin wasa na Old Trafford, inda Rashford ya ci kwallaye biyu.

A cikin minti shida da fara wasa ne dai Manchester United ta jefa kwallon farko a raga, a minti ma 39 kuwa Dele Alli ya farke wa Tottenham.

Ko da yake Mourinho ya amince ‘yan wasan sa ba su taka rawar gani ba, ya caccaki yadda ‘yan wasan United ke yawan faduwa kasa ko da ba a taba su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI