Wasanni-Kwallon kafa

Everton ta kori kocinta bayan shan kaye a hannun Liverpool

Marco Silva tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Everton.
Marco Silva tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Everton. Skysport.com

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sanar da korar kocinta Marco Silva watanni 18 bayan karbar ragamar fara korar da kungiyar, korar da ke zuwa sanadiyyar rashin katabus din da Everton ke nunawa a wasanninta na Firimiya cikin wannan kaka.

Talla

Korar ta Marco Silva dai baya rasa nasaba da ragargazar da Liverpool ta yiwa Club din a ranar Laraba inda ta ratata mata kwallaye har 5 da 2 matakin da ya mayar da ita ta 18 a teburin Firimiya da maki 14.

Shan kayen Everton a hannun Liverpool jagorar Firimiya ba sabon abu ba ne musamman ma idan ta yi tattaki zuwa Anfield, ko da dai ragargazar ta ranar laraba za a iya bayyanata a mafi muni da Everton ta fuskanta a gidan Liverpool.

Tun bayan karbar aikin Silva a watan Mayun bara, cikin wasanni 60 da ya jagoranci Club din ya yi nasara ne a guda 24 ya kuma yi rashin nasara a wasu 24 din yayin da ya yi canjaras a wasanni 12.

Yanzu haka dai tsohon mai tsaron gaba na Club din Duncan Ferguson ne zai jagoranci wasannin Club din ciki har da wanda Everton za ta kara da Chelsea a ranar Asabar, gabanin daukar sabon mai horarwa inda ake saran Everton ta maye gurbin Silva da Vitor Pereira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI