Wasanni-Kwallon kafa

Messi ya koka da yadda Mane ya kare a matsayin na 4 a Ballon d'Or

Dan wasan gaba na Liverpool Sadio Mané.
Dan wasan gaba na Liverpool Sadio Mané. Bulent Kilic / AFP

Dan wasan gaba na Barcelona da ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana Lionel Messi ya bayyana cewa babban abin kunya ne yadda dan wasan gaba na Liverpool Sadio Mane ya kare a matsayin na 4 a jadawalin ‘yan wasan da suka shiga takarar lashe kyautar cikin makon nan.

Talla

Messi wanda wannan ne karo na 6 da ya lashe kyautar ta Ballon d’Or ya doke Virgil van Dijk na Liverpool a matsayin na 2 kana Cristiano Ronaldo na Juventus a matsayin na 3 sannan Sadio Mane daga Liverpool a matsayin na 4 yayinda Mohammed Salah shima daga Liverpool din ya zo a matsayin na 5.

Messi dan Argentina mai shekaru 32 ya ce ko yayin zaben dan wasan mafi hazaka na bana da FIFA ta gudanar Mane ya zaba, don a tunaninshi babu dan wasan da ya kai shi, amma kuma bai kamata ace yak are ana 4 yayin kyautar Ballon d’Or ba.

A cewar Messi Sadio Mane babban jigo ne ga ilahirin tawagar Liverpool wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kai club din ga nasararo.

Kusan dai za a iya cewa Manen ya tabbatarwa duniya hakan a wasanni daban-daban ciki har da na baya-bayan nan da Liverpool ta lallasa Everton inda ya taimaka wajen zura kwallaye 3 yayinda ya zura 1 a karan kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI