Isa ga babban shafi
Wasanni

Wasanmu da Manchester City wata dama ce a gare mu- Solskjaer

Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer
Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer Reuters/John Sibley
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 1

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce, karan-battar da za su yi da Manchester City a gobe Asabar, wata dama ce da za su yi amfani da ita wajen sauya shakkun da ake da shi kan kungiyar zuwa kwarin guiwa.

Talla

Duk da cewa kungiyar ta Manchester United ta fara kakar bana mafi muni tun shekarar 1988, amma ta yi nasarar casa Tottenham a tsakiyar makon nan, inda kuma ta haura matsayi na shida a teburin gasar firimiyar Ingila.

Kodayake Solskjaer ya ce, karawarsu da Manchester City za ta yi zafi, amma suna bukatar ci gaba da nuna karsashi a cewarsa.

Kocin Manchester City shi ma ya ce, za su dauki wasan da muhimmanci duk da tazarar maki 11 da suka bai wa Manchester United a teburi.

Kungiyoyin biyu sun dade suna hamayya da juna a fagen tamaula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.