Wasanni

Emery na gaf da samun sabon aiki a gasar Premier

Tsohon kocin Arsenal Unai Emery.
Tsohon kocin Arsenal Unai Emery. © Action Images via Reuters/Paul Childs

Rahotanni daga Ingila na cewa kungiyar Everton ta tuntubi tsohon kocin Arsenal Unai Emery domin maye gurbin kocinta da ta kora Marco Silva.

Talla

Kafar yada labaran wasanni ta Sky Sports, ta ce tuni aka gana tsakanin wakilan kungiyar ta Everton ta Emery a birnin London.

Sai dai rahoton ya ce Emery ya nemi bashi karin lokaci kafin yanke shawara kan amincewa da kulla yarjejeniyar, kasa da makwanni 3 bayan sallamar shi da Arsenal ta yi.

Tun bayan korar kocinta Marco Silva da Everton ta yi, shugaban kungiyar Bill Kenwright ya bayyana sunayen manyan masu horaswa 4 da yake fatan kulla yarjejeniya da su, ciki har da kocin kungiyar Napoli Carlo Ancelotti, ba ya ga tsohon kocin na Arsenal Unai Emery.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI