Wasanni

Guardiola ya bayyana kungiyoyin da suka yiwa City zarra

Mai horas da 'yan wasan Manchester City Pep Guardiola.
Mai horas da 'yan wasan Manchester City Pep Guardiola. © REUTERS/Phil Noble

Kocin Manchester City Pep Guardiola, ya bayyana wasu kungiyoyi guda 5 wadanda ya ce ko shakkah babu, tasa kungiyar ba za ta iya yin gogayya da su ba.

Talla

Kungiyoyin da Guardiola ya zayyana kuwa sun hada da Barcelona, Real Madrid, Manchester United, Liverpool da kuma Juventus.

Kafin zuwan wannan lokaci dai, Manchester City dake karkashin Pep Guardiola ta shafe shekaru 2 a matsayin zakara kuma mafi kwazo a gasar Premier, wanda yasa a kakar wasa ta 2017/2018 kungiyar ta lashe gasar Premier damaki 100.

To sai dai a kakar wasa ta bana, bayan buga wasanni 16, yanzu haka Manchester City na kan matsayi na 3 da maki 32, maki 14 tsakaninta da Liverpool jogarar gasar ta bana mai maki 46.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI