Wasanni

WADA ta haramtawa Rasha shiga wasanni tsawon shekaru 4

Tutocin Rasha ba za su yi shawagi a wasanni daban daban ba tsawon shekaru 4, bayan kakaba mata takunkumin shiga gasanni.
Tutocin Rasha ba za su yi shawagi a wasanni daban daban ba tsawon shekaru 4, bayan kakaba mata takunkumin shiga gasanni. AFP/File / Kirill KUDRYAVTSEV

Hukumar yaki da shan kwayoyin karin kuzari ta duniya WADA, ta haramtawa Rasha shiga dukkanin nau’ikan wasanni a matakin duniya tsawon shekaru 4, saboda samun gwamnatin kasar da laifin boye gaskiyar sakamakon bincike kan batun tu’ammuli da kwayoyin karin kuzari ba bisa ka’aida ba, tsakanin ‘yan wasan kasar dake wakiltarta a gasanni.

Talla

Majalisar kolin hukumar ta WADA ta yanke hukuncin kan Rasha ne, yayin taro a birnin Lausanne dake Switzerland.

Takunkumin da hukumar WADA ta kakabawa Rasha na nufin kasar ba za ta shiga gasar wasannin motsa jiki ta duniya da za ta gudana a birnin Tokyo na Japan cikin shekara mai kamawa ba.

Zalika kasar ta Rasha, ba za ta shiga gasar kwallon kafa ta duniya da Qatar za ta karbi bakunci ba a 2022.

Wani karin matsi da wannan takunkumi ya laftawa Rasha, shi ne haramtawa jami’an gwamnatin kasar halartar dukkanin nau’ikan gasannin duniya, zalika daga yanzu har zuwa nan da shekaru 4, Rashar ba ta da ikon nema ko samun damar karbar bakuncin wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.