Wasanni-Kwallon kafa

Liverpool ta shirya karawa da Salzburg- Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Juergen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Juergen Klopp. REUTERS/Andrew Yates

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce sun shiryawa karawarsu Red Bull Salzburg karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Talla

Zakarar ta Turai wadda ta lallasa Salzburg cikin watan Oktoba a Anfield da kwallaye 4 da 3, duk da kasancewarta jagora a rukunin E har yanzu ta na bukatar maki daga waje la’akari da cewa dukkannin wasanninta da ta yi nasara sun gudana ne a gidanta.

Matukar dai ta yi nasara a wasamn na yau kai tsaye zakarar ta Turai ta samu gurbi a zagayen kungiyoyi 16

A taron manema labaran da ya kira game da wasan Jurgen Klopp ya ce a shirye suke su tunkarar tawagar ta Salzburg can a Austria, domin basu karaya ba za su dukkan kokari wajen ganin sun sake kaiwa ga matakin lashe kofin a wannan karonma.

Sai dai Liverpool za ta kara wasan nay au ne ba tareda dan wasanta na tsakiya Adam Lallana ba, ko da dai Klopp ya bada tabbacin kasancewar Dejan Lovren da Gini Wijnaldum a tsakiyar.

Ko da ace Salzburg ta yi nasara a wasan na yau Liverpool za ta iya sa rai a zuwa rukunin kungiyoyi 16 idan har Genk ta lallasa Napoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI