Wasanni

Kungiyoyin Ingila na zawarcin Neymar da Mbappe

Neymar da Kylian Mbappé
Neymar da Kylian Mbappé FRANCK FIFE / AFP

Jaridar Le Parisien ta Faransa ta rawaito cewa, Liverpool da Manchester City da Chelse na cikin kungiyoyi shida da suka nuna sha’awarsu ta sayo Neymar da Kylian Mbappe daga PSG ta Faransa.

Talla

Har yanzu, Neymar na Brazil na hangen ficewarsa daga PSG, yayin da Jaridar Marca ta ce, Mbappe ba shi da aniyar sabonta kwantiraginsa da PSG wanda zai kare a shekarar 2022.

A bangare guda, PSG na zawarcin Sadio Mane na Liverpool, inda take fatan kulla kwantiragi da shi da zaran ta raba gari da Neymar.

Jaridar Sport Witness ta ce, Mane na ci gaba da samun farin jinni a wurin mahukuntan PSG.

Sai dai babu tabbas ko Mane da Liverpool za su amince da wannan tayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.