Wasanni

Matashin dan wasan Barcelona ya kafa tarihi

Matashin dan wasan Barcelona, Ansu Fati ya kafa tarihin zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya jefa kwallo a raga a gasar cin kofin zakarn Turai.

'Yan wasan Barcelona sun taya Ansu Fati murnar jefa kwallo a ragar Inter Milan
'Yan wasan Barcelona sun taya Ansu Fati murnar jefa kwallo a ragar Inter Milan Daniele Mascolo/Reuters
Talla

A minti na  85 aka sanya Fati mai shekaru 17 cikin wasan da Barcelona ta doke Inter Milan da ci 2-1, inda a minti na 86 ya ci wa kungiyarsa kwallo ta biyu bayan Luiz Suarez ya taimaka masa.

Barcelona ta haramta wa Inter Milan samun gurbi a matakin kungiyoyi 16 sakamakon casa ta da ta yi a ranar Talata.

Tuni ita Barcelona ta samu gurbi a zagayen gaba na gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI