Napoli ta kori Ancelotti bayan ya taimaka mata
Wallafawa ranar:
Napoli ta kori kocinta Carlo Ancelotti kasa da sa’o’i uku da jagorantar kungiyar wajen samun nasarar tsallakawa matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun Turai.
Kungiyar wadda ke taka leda a gasar Serie A ta Italiya, ta gaza samun nasara a wasanni tara da ta buga, amma a ranar Talata ta samun nasarar doke Genk da kwallaye 4-0 a gasar zakarun Turai, abin da ya ba ta damar samun gurbin.
Kungiyar na a matsayi na bakwai a teburin gasar Serie A da maki 21, inda Inter Milan da ken jan ragamar teburin ta ba ta tazarar maki 17 .
Rahotanni na cewa, tsohon kocin AC Milan Gennaro Gattuso ne zai maye gurbin Ancelotti a Napoli
Tuni Everton ta fara kallon Ancelotti a matsayin babban zabinta na kocin da zai maye gurbin Marco Silva da ta raba gari da shi.
Ancelotti ya lashe kofunan zakarun Turai har guda uku a matsayin koci, daya da Real Madrid, sai kuma biyu da AC Milan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu