Kingsley na Bayer Munich zai yi jinyar rauni
Wallafawa ranar:
Kungiyar kwallon kafa ta Bayer Munich ta ce babu abin fargaba tattare da raunin Kingsley Coman bayan da ta yi nasara kan Tottenham da kwallaye 3 da 1 tare da kammala wasanninta na rukuni a matsayin jagora da maki 18.
Coman wanda ya samu rauni a gwiwa bayan nasararsa ta zura kwallo guda a farkon wasan na jiya, Club din ya ce raunin nasa ba abin tayar da hankali ba ne, domin kuwa akwai yiwuwar ya murmure cikin sauri.
Sanarwar da Club din ya fitar ta nuna cewa Coman dan Faransa mai shekaru 23 zai murmure tare da tunkarar wasannin da ke gaban Club din a zagayen kungiyoyi 16 na cin kofin zakarun Turai dama wasannin Bundesliga.
Bayern Munich dai ita ce kungiyar kwallon kafa daga Jamus daya tilo da ta nasara a wasanninta 6 na rukuni karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu