Manchester United za ta raba gari da Pogba
Wallafawa ranar:
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara shirye-shiryen raba gari da Paul Pogba mai yiwuwa a kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu bayan tsanantar bukatar hakan daga dan wasan da kuma Real Madrid.
Tun cikin watan Yunin da ya gabata ne, Pogba ya fito karara ya nuna bukatar raba gari da Red Devils yayinda Zinadine Zidane ya nuna bukatar dan wasan a Real Madrid ko da dai takaddama kan farashi ta sa aka rabu da cinikin baram-baram bayan da United ta sa farashin Yuro miliyan 160 kan dan wasan.
Sashen wasanni na jaridar Daily Mail ya bayyana cewa Tuni United ta fara shirye-shiryen sayo ‘yan wasan da za sum aye gurbin Pogba ciki kuwa har da Saul Niguez na Atletico Madrid da James Maddison na Lesta City.
Pogba dan Faransa wanda ya yi ta gamuwa da raunuka a wannan kaka, tun daga watan Agusta wasanni 5 kacal ya samu bugawa United saboda jinya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu