Klopp ya tsawaita kwantiraginsa da Liverpool

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. Reuters

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa wanda zai kaishi har nan da shekarar 2024.

Talla

Klopp wanda ya fara aiki da Reds cikin watan Oktoban 2015 a watan Yulin 2016 ne ya tsawaita kwantiraginsa zuwa shekaru 5 kafin a yau ya sake tsawaitawa zuwa wasu shekaru 5 din masu zuwa.

A bara dai Klopp ya kai Liverpool ga dage kofin zakarun Turai yayinda ya kai ta matsayin ta biyu a Firimiya banbancin maki daya tsakaninta da mai rike da kambu Manchester City.

Da ya ke jawabi ga manema labarai, Klopp dan Jamus mai shekaru 52 ya ce nasarar Liverpool aiki ne na hadin gwiwa ba wai shi daya ya cancanci jinjina ba, kuma ya na fatan ya ci gaba kamar yadda aka faro.

Yanzu haka dai Liverpool na kan hanyar lashe kofin Firimiya bayan da ta doka wasannin rabin gasar Firimiya tana matsayin jagora da tazarar maki 8 tsakaninta da mai bi mata Lesta City, kuma matukar ta yi nasarar dage kofin a wannan karon zai kawo karshen dakonta na shekaru 30 ba tare da kofin yaje gidanta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.