Wasanni

Arsenal ta tuntubi Arteta

Mikel Arteta tare da Pep Guardiola.
Mikel Arteta tare da Pep Guardiola. Getty Images

Hukumar gudanarwar Arsenal ta cimma matsayar zabar tsohon dan wasanta Mikel Arteta a matsayin sabon kocin kungiyar.

Talla

Yanzu haka dai Arteta na rike da mukamin mataimakin kocin kungiyar Manchester City Pep Guardiola.

Kafar yada labaran wasanni ta Sky Sports ta rawaito cewar tuni wakilan Arsenal suka yi tattaki zuwa gidan Arteta, inda suka soma tattaunawa don kulla yarjejeniya da shi, jim kadan bayan wasan gasar Premier da Manchester City ta lallasa Arsenal din da kwallaye 3-0 a ranar lahadi.

A makon jiya Arsenal ta salami kocinta Unai Emery, sakamakon durkushewar da karsashin kungiyar yayi, mafi muni cikin kusan shekaru 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.