Wasanni

Messi ya lashe karin kyautukan yin zarra a duniyar kwallo

Lionel Messi.
Lionel Messi. Susana Vera/Reuters

Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon shekara na gasar La Liga, yayin bikin bada kyautukan jaridar wasanni ta Marca ta jagoranta a daren jiya litinin.

Talla

Yayin bikin karrama ‘yan wasan, Messi ya kuma karbi kyautar Pichichi ta takalmin Zinare, bayan yiwa takwarorinsa na la liga zarra wajen cin kwallaye a kakar wasa ta bara.

Kaftin din na Barcelona bai samu halartar bikin bada kyautukan ba, sai dai ta sakon bidiyon da aike zuwa taron, yayi godiya da kuma bayyana amincewa da karramawar.

Karin kyautakn da Messi ya lashe a gasar La Liga, sun zo ne bayan da ya lashe kyautukan gwarzon dan wasan duniya na FIFA da kuma Ballon d’Or.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI