Wasanni

'Yan wasan Arsenal sun karkata ga Ancelotti

Tsohon mai horas da kungiyar Napoli Carlo Ancelotti.
Tsohon mai horas da kungiyar Napoli Carlo Ancelotti. REUTERS/Ciro De Luca

Wata majiya daga Arsenal ta ruwaito cewar mafi akasarin ‘yan wasan kungiyar sun fi karkata kan ra’ayin daukar tsohon kocin Napoli Carlo Ancelotti a matsayin sabon mai horas da su.

Talla

Rahoton na jaridar UK Mirror ta wallafa, ya zo a dai dai lokacin da wakilan kungiyar ta Arsenal suka tuntubi tsohon dan wasansu Mikel Arteta, wanda a yanzu yake mataimakin kocin kungiyar Manchester City Pep Guardiola.

Wasu daga cikin ‘yan wasan na Arsenal na da ra’ayin Ancelotti yafi Arteta cancanta da kwarewa saboda tarihinsa na horas da kungiyoyin Chelsea, Real Madrid, Juventus da kuma Paris Saint-Germain, shi kuwa Arteta mataimakin koci ne tun bayan yin ritaya daga kwallon kafa a Arsenal.

Muhawara tsakanin ‘yan wasan kungiyar ta Arsenal na zuwa ne, yayinda rahotanni ke cewa tsohon kocin na Napoli wato Ancelotti ya amince da tayin karbar aikin horas da kungiyar Everton, kamar yadda kafar labaran wasanni ta Sky Sports ta ruwaito.

Sai dai kungiyar ta Everton ta fitar da sanarwar cewa har yanzu ba ta cimma matsaya kan sabon kocin da za ta dauka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI