Wasanni-Kwallon kafa

Arsenal ba ta tuntubemu game da Arteta ba - Man City

Har yanzu Manchester City da Arsenal ba su kai ga tattauna batun biyan hakkokin da za su kai ga cimma yarjejeniyar dauko mataimakin kocinta Mikel Arteta don ya maye gurbin Unai Emery ba.

Mikel Arteta da Pep Guardiola. ( Getty Images )
Mikel Arteta da Pep Guardiola. ( Getty Images ) Getty Images
Talla

Rahotani na nuni da cewa Arsenal na ta kokarin ganin ta dauko dan shekara 37 din don ya ci gaba da horar da ‘yan wasanta bayan hannun riga da ta yi da Emery.

A daren Laraba Arteta ya yi tattaki zuwa Oxford tare da ‘yan wasan City a karawar da suka yi a wasan kofin Carabao, kuma dai a nan gaba a wannan mako ake sa ran Arsenal ta nada shi a matsayin kocinta.

Sai dai hankalin hukumomi a Mancheser City ya tashi ganin yadda Arsenal din basa yin abin da ya dace wajen cinikin mai horarwar.

Kuma har yanzu babu wata tattaunawa a hukumance tsakanin kungiyoyin biyu game da Arteta, kuma ba a kai ga cika ka’idodin dauko mai horarwar ba.

Majiyoyi daga Manchester City na cewa, kungiyar na matukar mamaki jin cewa Arsenal tana shirye - shiryen gabatar da Arteta a matsayin mai hoorar da ‘yan wasan ta a wannan Juma’ar.

Da yake bayani bayan wasan da City ta doke Oxford 3-1, mai horar da ‘yan wasan City Pep Guardiola ya ce shi dai har yanzu tare suke aiki da Arteta, kuma tare suke shirya wa wasanni kullayaumin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI