Arsenal za ta gabatar da Arteta a matsayin kocinta Juma'ar nan
A yau Juma’a ake saran kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta gabatar da Mikel Arteta a matsayin mai horar da ‘yan wasanta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A ranar Alhamis Arteta ya yi bankwana da abokan aikinsa a Manchester City sakamakon wannan aiki da ya samu na horarwa a filin wasa na Emirates.
Hukumomi a Manchester City dai sun bayyana rashin jin dadinsu game da abin da suka kira ‘kin bin ka’ida’ daga Arsenal, amma hakan ba zai hana Arteta mai shekaru 37 maye gurbin Unai Emery ba.
Kocin wucin – gadi, Freddie Ljungberg ne zai jagoranci wasan Arsenal daEverton a Goodison Park a gobe Asabar, inda Arteta zai kasance amma amatsayin dan kallo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu