Wasanni-Kwallon kafa

Arteta ya zama sabon Kocin Arsenal

Mikel Arteta tare da Pep Guardiola.
Mikel Arteta tare da Pep Guardiola. Getty Images

Tsohon mataimakin mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Mikel Arteta, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara 3 da rabi don jan ragamar horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke matsayin tsohon Club dinsa.

Talla

Arteta mai shekaru 37 wanda ya bugawa Arsenal wasanni fiye da 100 tsakanin shekarun 2011 zuwa 2016 lokacin da ya yi ritaya daga kwallo, zaimaye gurbin Unai Emery da Arsenal ta kora daga aiki cikin watan jiya sakamakon gazawar Club din wajen lashe manyan wsanni cikin har da wadanda aka ragargajeta a gida.

Yanzu haka dai wasa 1 cal cikin wasanni 12 Arsenal ta iya nasarar lashewa, yayinda wasan da Arteta zai fara jagoranta zai kasance mai cike da kalubale la’akari da yadda zai yi tattaki zuwa Everton da ke matsayin guda cikin tsaffin Club din da ya taka leda a zamanin kuruciyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.