Wasanni-Kwallon kafa

Rashin hankali na ta'azzara wariya a kwallon kafa - Toure

Yaya Toure
Yaya Toure Reuters

Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester City, dan kasar Ivory Coast, Yaya Toure ya ce tsabagen karuwar rashin hankali daga magoya baya ne ya tsananta matsala wariyar launin fata a kwallon kafa.

Talla

An ruwaito batutuwa da suka shafi wariyar launin fata a ‘yan watannin baya a kafafen yada labarai, inda mafi akasari masu munin cikinsu sun auku ne a gasar Seria A ta Italiya.

Toure ya ce ya gana da hukumar kwallon kafa ta duniya kan wannan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa a harkar kwallon kafa, sai dai zai yi wuya matsalar ta kau gaba daya duba da yadda gidadanci ke karuwa a tsakanin magoya bayan wasan kwallon kafa.

A watan da ya gabata, Mario Balotelli, tsohon abokin wasan Toure ya bayyana wasu magoya baya da suka nuna mai wariya a wasa tsakanin Brescia da Verona a matsayin ‘kananan mutane’ kuma ‘marasa hankali’.

Magoya bayan Cagliari sun yi wa dan wasan gaban Inter Milan, Romelu Lukaku kukan birrai a farkon wannan kaka, sannan kuma ba da dadewa ba jaridar Corriere dello Sport da ake wallafawa a Italiya ta sha suka saboda wani labarin ta mai taken ‘Black Friday’, wato ‘Bakar Juma’a’, inda ta yi amfani da hotunan Lukaku da Chris Smalling, wadanda dukkanninsu bakar fata ne.

Toure ya ce akwai yara da ke tasowa, bai kamata a bari su koyi wannan bakar dabi’ar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.