Wasanni-Kwallon kafa

Van Dijk na da lafiyar taka leda a wasan Club World Cup- Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce suna da kyakkyawan fatan mai tsaron baya na Club din Virgil van Dijk zai kammala murmurewa gabanin karawarsu ta gaba a gobe asabar karkashin gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi wato Club world Cup.

Mai tsaron baya na Liverpool Virgil van Dijk.
Mai tsaron baya na Liverpool Virgil van Dijk. Reuters
Talla

A cewar Klopp ko a yau Juma’a van Dijk ya shiga filin atisayen tunkarar wasan na gobe da za su kara da Flamengo ta Brazil wanda zai fayyace bangaren da zai dage kofin na bana.

Baya ga wasan ranar Laraba da Liverpool ta lallasa Monterrey ta Mexico da kwallaye 2 da 1 a matakin wasan gab da na karshe, Van Dijk bai rasa ko da guda cikin wasannin Club din a wannan kaka ba.

Kafin dai kalaman na Klopp a wannan yammaci, magoya bayan Liverpool na cike da fargabar yiwuwar taka ledar mai tsaron bayan, musamman ganin yadda Joel Matip, Fabinho da Dejan Lovren baza su taka leda a wasan ba, ko da dai dama Klopp ya bayyana cewa zai yi amfani da Jordan Henderson da Joe Gomez don bayar da tsaro a tsakiya.

Ka zalika Georginio Wijnaldum shima da ke fama da rauni Klopp ya ce akwai yiwuwar ya taka leda a wasan na gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI