Wasanni-Kwallon kafa

Ancelotti da Arteta na da jan aiki a gabansu

An yi wa Carlo Ancelotti da Mikel Arteta nuni da gagarumin aikin da ke gabansu a matsayinsu na maso horar da ‘yan wasan Arsenal da Everton, bayan kungiyoyin biyu sun buga canjaras babu ci a wasan da suka fafata a Goodison Park.

Mikel Arteta da Carlo Ancelotti
Mikel Arteta da Carlo Ancelotti Reuters
Talla

A safiyar Asabar din ne aka tabbatar da Ancelotti a matsayin mai horar da Everton, sa’o’i 24 kenan bayan Arsenal ta gabatar da Mikel Arteta a matsayin kocinta.

Dukannin sabbin masu horarwan sun shiga filin da aka fafata ne a matsayin ‘yan kallo yayin da Duncan Ferguson ya jagoranci Everton, Freddie Ljungberg kuma ya ja ragamar Arsenal, duk a matsayin kocawan wucin – gadi.

Wasan dai bai yi armashi ba, saboda dalilin da ya sa aka bar kungiyoyin biyu a baya ya bayyana karara a karawar da ‘yan wasan suka yi ba karsashi.

Arsenal tana matsayi na 9 a teburin gasar Firmiyar Ingila, kuma a duka gasanni, sau daya ta samu nasara a wasanni 13.

Everton ta hau matsayi na 15, amma maraban su da kungiyoyin da ke rikitowa maki 4 ne kacal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI