Wasanni-Kwallon kafa

Ibrahimovic ya koma AC Milan

Zlatan Ibrahimovic sanye da kayan wasan Manchester United
Zlatan Ibrahimovic sanye da kayan wasan Manchester United Reuters / Eddie Keogh Livepic

Shahararren dan wasan kwallon kafa, dan kasar Sweden, Zlatan Ibrahimovic ya kulla yarjejeniya da kungiyar AC Milan, tsohuwar kungiyarsa, don murza mata tamaula ta tsawon watanni 6.

Talla

Ibrahimovic ya amince da tayin Milan, kuma nan ba da jimawa ba zai sanya hannu a yarjejeniya da kungiyar.

Ibrahimovic zai sanya hannu a kwantiragin watanni shida da aka kiyasta cewa ya kai Yuro miliyan 3 da dubu dari 3, da kuma zabin sabantawa da zai kai na shekara guda, idan ya buga wasanni dayawa ko kuma ya ci kwallaye.

Dan wasan mai shekaru 38 ya tabbatar da yin hannun riga da kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles Galaxy a watan da ya gabata, biyo bayan rikitowar da ta yi daga gasar Major League Soccer ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI