Wasanni-Kwallon kafa

Zlatan ya sake kulla kwantiragi da AC Milan

Zlatan Ibrahimovic.
Zlatan Ibrahimovic. Alessandro Garofalo/Reuters

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta tabbatar da kulla sabon kwantiragi tsakaninta da tsohon dan wasanta Zlatan Ibrahimovic wanda kwantiraginsa yak are da LA Galaxy cikin watan nan kuma yaki amincewa da sabunta kwantiragin.

Talla

Cikin sanarwar da AC Milan ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce yanzu haka sun kulla kwantiragin watanni 6 ne da dan wasan yayinda ya ke da cikakken zabin tsawaitawa ko akasin haka.

A sakon da ya wallafa a shafin Club din Ibrahimovic mai shekaru 38 ya ce abin alfahari sake dawowa take leda a AC Milan kuma zai dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun kai club din ga ci a wannan kaka.

Yanzu haka dai AC Milan ita ce matsayin ta 11 a teburin Serie A bayan shan kayenta da kwllaye 5 da banza a hannun Atalanta, shan kayen da ke matsayin mafi muni da Club din ya fuskanta cikin shekaru 21.

Cikin shekaru 2 da Zlatan ya shafe a AC Milan tsakanin shekarar 2010 zuwa 2012 ya yi nasarar zura mata kwallaye 42 a wasanni 61.

A italiya dai Zlatan ya taka leda a kungiyoyi irinsu Inter Milan inda y adage kofuna 2 a can sai kuma Juventus inda nan ma y adage kofi guda amma kuma dukkanninsu y araba gari dasu biyo bayan takaddamar da ta faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.