Wasanni-Kwallon kafa

West Ham ta dawo da Moyes fagen horar da 'yan wasanta

David moyes sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United.
David moyes sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United. Skysport.com

David Moyes ya sake karbar ragamar horar da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United kwantiragin da ke zuwa bayan korar Manuel Pellegrini da West Ham ta yi biyo bayan shan kayen Club din a wasanni 4 da ta karbi bakonci cikin gidanta ciki har da shan kayenta hannun Leicester da kwlalaye 2 da 1 a ranar Asabar.

Talla

Moyes wanda wannan ne karo na biyu da zai ja ragamar Club din a matsayin mai horarwa ya rattaba hannu kan kwantiragin watanni 18 ne, inda zai jagoranci wasan farko da Club din zai karbi bakoncin Bounermouth a ranar sabuwar shekara.

Moyes tsohon Kocin Everton da Manchester United wanda kuma ya yi nasarar daga darajar Club din a gasar Firimiya yayin kwantiraginsa na farko a shekarar 2017, ya ce ya karbi ragamar Club din a wani yanayi na koma baya, inda yanzu haka yake matsayin na 17 da maki 19 bayan doka wasanni 19, wato dai gab da shiga rukunin hadari a teburin na Firimiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI