Aguero ya sake kafa tarihi a gasar Premier
Wallafawa ranar:
Mai horas da Manchester City Pep Guardiola, ya jinjinawa dan wasansa na gaba, Sergio Aguero bisa bajintar jefa kwallo a ragar abokan hamayya, fannin da dan wasan ke ci gaba da nuna zarra a tsakanin takwarorinsa dake wasa a gasar Premier ta Ingila.
A lokacin da yake yabawa dan wasan nasa Guardiola ya ce akwai alamun Aguero ba zai daina zura kwallaye a ragar abokan hamayya ba har sai bayan mutuwarsa.
A ranar lahadi 12 ga Janairun 2020, Manchester City ta lallasa Aston Villa da kwallaye 6-1, wanda kuma Aguero ne ya ci 3 daga ciki.
Bajintar dan wasan daga Argentina ne kuma ta bashi damar kafa sabbin tarihai har kashi 2 a gasar ta Premier Ingila.
Tarihi na farko dai shi ne zarta bajintar zura kwallo mafi yawa a Ingila da wani dan wasa daga wata kasa ya kafa, wanda a baya Thiery Henry Bafaranshe ya kafa a Arsenal.
Tarihi na 2 da Aguero ya kafa kuwa shi ne goge bajintar da Alan Shearer ya kafa na dan wasan dake kan gaba a adadin zura kwallaye 3 a wasa 1 karo daban daban har sau 11, wato Hattrick.
A halin yanzu Aguero na da adadin kwallaye 3 a wasa guda sau 12 bayan wasan da ya zurawa Aston Villa kwallaye 3 a raga, abinda ya bashi damar ci wa kungiyarsa ta Manchester City jimillar kwallaye 177, bayan soma buga mata wasanni a 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu