Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta yi ikirarin iya lallasa Liverpool har gida

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer. Reuters/Andrew Boyers
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi ikirarin iya kawo karshen jerin gwanon nasarar da Liverpool ke yi karkashin gasar Firimiya, bayan da United ta bayyana kanta a matsayin Club guda da ka iya nasara kan Liverpool har gidanta yayin wasansu na ranar Lahadi mai zuwa.

Talla

Manajan na Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne, nasarar United kan Reds idan aka yi la’akari da yadda kungiyoyin biyu suka yi canjaras da kwallo 1-1 cikin watan Oktoba.

Sai dai duk da kasancewar United a matsayin babbar abokiyar dabin Liverpool, ba lallai kalaman na Solsha su zama gaskiya ba, la’akari da cewa Liverpool din wadda rabon da ta yi rashin nasara a wasa tun cikin watan Janairun bara a hannun Manchester city, yanzu haka ta na shirin doka wasa na 38 ne ba tare da anyi nasara kanta ba karkashin gasar ta Firimiya yayinda take matsayin jagora da maki 61 bayan doka wasanni 21, dalilan da ke nuna cewa abu ne mai wuya United din ta iya samun nasara a wasan.

Liverpool da ke matsayin zakarar Turai a yanzu kuma wadda ta dage kofin gasar cin kofin duniya na kungiyoyi a baya-bayan nan, rabon da ta yi rashin nasara a wasan da ta karbi bakoncin cikin Anfield tun watan Aprilun 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.