Wasanni

Osimhen ya shiga jerin zakakuran maciya kwallo a Turai

Dan wasan Najeriya a tawagar Super Eagles, Victor Osimhen dake kungiyar Lille a kasar Faransa.
Dan wasan Najeriya a tawagar Super Eagles, Victor Osimhen dake kungiyar Lille a kasar Faransa. Yahoo News

Dan wasan Najeriya dake kungiyar Lille a gasar Ligue 1 ta Faransa Victor Osimhen, ya dare kan matsayi na 4 a tsakanin matasan dake wasa a nahiyar Turai, ‘yan kasa da shekaru 23, wadanda ke kan gaba wajen cin kwallaye.

Talla

Yanzu haka dai Osimhen ya ciwa kungiyarsa ta Lille kwallaye 10 a kakar wasa ta bana, adadin kwallaye guda da dan wasan gaba na Inter Milan Lautaro Martinez na kasar Argentina ke da su.

Marcos Rashford na Manchester United ke kan gaba tsakanin maciya kwallayen matasa ‘yan kasa da shekaru 23 dake taka leda a kungiyoyin Turai, inda a kakar wasa ta bana yake da 14.

Biye da Rashford kuma dan wasan gaba na Chelsea ne Tammy Abraham da kwallaye 13, sai kuma Kylian Mbappe na kungiyar PSG a matsayi na 3 da kwallaye 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI