Manyan kungiyoyin Turai na rige-rigen sayen Osimhen
Wallafawa ranar:
Kungiyar Sevilla ta bi sawun takwarorinta na Barcelona da Real Madrid da kuma wasu kungiyoyi dake gasar Premier Ingila, wajen rige-rigen kulla yarjejeniya da dan wasan Najeriya na tawagar Super Eagles, Victor Osimhen dake kungiyar Lille a Faransa.
A halin yanzu dai Victor Osimhen ne dan wasa na uku mafi daraja a gasar Ligue 1 ta Faransa ajin matasa, kuma a baya bayan nan dan wasan ya dare kan matsayi na 4 a tsakanin matasan dake wasa a nahiyar Turai, ‘yan kasa da shekaru 23 dake kan gaba wajen jefa kwallaye a raga.
Yanzu haka dan wasa ya ciwa kungiyarsa ta Lille kwallaye 10 a kakar wasa ta bana, adadin kwallayen da dan wasan gaba na Inter Milan Lautaro Martinez ke da su.
Marcos Rashford na Manchester United ke kan gaba tsakanin zakakuran matasan ‘yan kasa da shekaru 23 a kungiyoyin Turai, inda a kakar wasa ta bana yake da kwallaye 14. Sai kuma dan wasan gaba na Chelsea ne Tammy Abraham da kwallaye 13, sai kuma Kylian Mbappe na kungiyar PSG a matsayi na 3 da kwallaye 11.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu