Wasanni-Kwallon kafa

Lampard na bukatar Cavani a Chelsea

Dan wasan PSG, Edinson Cavani
Dan wasan PSG, Edinson Cavani REUTERS/Charles Platiau

Bukatar dan wasan gaba na kasar Uruguay Edinson Cavani na barin kungiyarsa ta PSG ta ja hankalin kocin Chelsea Frank Lampard, wanda ya nuna takaici kan yadda ‘yan wasansa ke kamfar cin kwallaye.

Talla

Duk da cewa dan wasan gaba na Chelsea, Tammy Abraham ya ci kwallaye 16 a dukkan gasanni a wannan kaka, Lampard ya kwana da sanin cewa yana neman wanda zai tallafa wa dan wasan wajen saka kwallaye a raga.

Ci daya mai ban haushi da Newcastle ta yi wa Chelsea a ranar Asabar da ta gabata ya nuna rashin karsashin ‘yan wasan kungiyar wajen cin kwallaye.

Chelsea wacce ke matsayi na 4 a teburin gasar Firimiyar Ingilar za ta fafata da Arsenal a yau Talata, kuma ratar maki 5 ne ta baiwa Manchester United da Wolverhampton Wanderers.

Cavani ne dan wasan da ya fi ci wa PSG kwallaye, inda yake da kwallaye 198, amma dan wasan wanda sau 116 ya buga wa kasarsa wasa, ya shaida wa kungiyarsa cewa yana sha’awar komawa Atletico Madrid ta kasar Spain.

Da jin haka Lampard ya nuna sha’awar kawo dan wasan gaban mai shekaru 32 Stamford Bridge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.