Wasanni

Mourinho na son karbar aron Mbappe daga PSG

Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG.
Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG. Charles Platiau/Reuters

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Jose Mourinho ya ce kofa a bude ta ke ga Christian Eriksen da ke kokarin raba gari da Club din zuwa Inter Milan, yayinda manajan ke cewa za su so ganin Kyllian Mbappe a Club din.

Talla

Kalaman na Mourinho na zuwa dai dai lokacin da jita-jitar sauya shekar Mbappe zuwa Real Madrid ke kara yaduwa.

A cewar Mournho ba ko da yaushe ne za su yi ta sayen ‘yan wasa ba, amma zai so PSG ta amince da basu Mbappe a matsayin aro.

Mourinho wanda ya ki cewa komai game da tambayar da aka yi masa kan yiwuwar Tottenham ta sayi Edinson Cavani shima dai dan wasan PSG, ya ce akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakaninsa da shugabancin PSG kuma zai yi fatan su amsa bukatarshi.

A wani labarain na daban kuma, Dan wasan gaban na PSG Kyllian Mbappe yayin zantawarsa da jaridar wasanni a Faransa, ya ce yana farin ciki da inda ya ke yanzu a fagen kwallo, amma idan har akwai Club din da zai taka leda a Ingila bai wuce Liverpool ba.

Jita-jitar bukatar Mbappe a Liverpool dai ta mutu ne bayan da Jurgen Klopp ya bayyana cewa Club din bashi da kudin sayo dan wsaa daga PSG.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI