Wasanni

Mutuwar Kobe Bryant ta girgiza fitattun mutane a duniya

Marigayi Kobe Bryant ya bayar da gagarumar gudunmawa a duniyar kwallon kwando
Marigayi Kobe Bryant ya bayar da gagarumar gudunmawa a duniyar kwallon kwando REUTERS/Lucy Nicholson

Fitaccen tsohon dan wasan kwallon kwando dan asalin Amurka, Kobe Bryant da ’yarsa na cikin mutane 9 da suka gamu da ajalinsu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungula a birnin Calabasas da ke California, yayin da fitattun mutane a bangarori daban daban suka bayyana kaduwarsu.

Talla

Bryant mai shekaru 41 na kan hanyarsa ta zuwa kallon wani wasan kwallon kwando yayin da karamin jirgin ya rikito tare da kamawa da wuta.

Bryant wanda ya lashe kambun gasar NBA har sau biyar, ya shafe tsawon shekaru 20 yana buga wa kungiyar Los Angeles Lakers wasanni, kuma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin zaratan ‘yan wasan da tarihin kwallon kwando ba zai manta da su ba.

A cikin watan Afrilun shekarar 2016 ne ya yi ritaya daga buga kwallon kwando.

Tuni fitattun mutane da takwarorinsa suka aika da sakwannin ta’aziya, inda suka bayyana kaduwarsu da mutuwarsa, yayin da aka yi shiru na wani dan lokaci a daukacin wasannin kwallon kwando a Amurka domin karramawa ga marigayin.

Cikin wadanda suka aike da sakon ta’aziya har da shugaban Amurka, Donald Trump da tsohon shugaban kasa Barack Obama da Michael Jordan da Shaquille O’Neal da Malik Abdeljabaar.

Sauran sun hada da Tiger Woods da Manny Pacquiao da Neymer, yayin da dubban magoya bayansa suka yi gangami a titunan Los Angeles, birnin da ya kwashe shekaru 20 yana yi wa wasa.

Da dama daga cikin ‘yan wasan da ke buga gasar NBA sun ce, sun rasa kuzarin shiga filin wasa saboda wannan rashin.

Hukumar Gasar NBA ta fitar da sanarwa inda take cewa, ta razana da mutuwar Bryant da ‘yarsa, Gianna mai shekaru 13.

Wasu shaidu sun bayyana cewa, jirgin ya yi ta kara tun a  sararin samaniya kafin ya rikito, yayin da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Amurka ta tashi tawaga ta musamman domin gudanar da bincike kan musabbabin hadarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI