Wasanni-Kwallon kafa

Messi zai karasa sana'arsa a Barcelona - Guardiola

Lionel Messi dan wasa Barcelona da Argentina.
Lionel Messi dan wasa Barcelona da Argentina. REUTERS/Waleed Ali

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ruguza rade radin da ake cewa Lionel Messi zai koma kungiyar da yake horarwa, wato Manchester City, inda ya ce yana da yakinin dan wasan zai karasa sana’arsa ta murza tamola a Barcelona.

Talla

Messi, mai shekaru 32 ya shafe ilahirin shekarun sana’arsa ta kwallon kafa a Barcelona, sai dai a yarjejeniyarsa na yanzu, yana da damar barin kungiyar a karshen kakar nan da muke ciki.

Guardiola ya horar da Messi a tsakanin shekarar 2008 zuwa 2012 a Barcelona, inda tare suka lashe kofunan Laliga 3 da na zakarun nahiyar Turai 2.

Tsohon kocin na Barcelona ya ce fatarsa ita ce Messi ya ci gaba da zama a Barcelona.

Guardiola wanda ya bar Barca zuwa Bayern Munich bayan ya kasance kocin da ya fi kowane koci samun nasarori da kofuna 14 a kaka 4.

Daga nan ya lashe kofin Bundes Liga 3 a jere da Bayern Munich, sannan a kakani 2 ya lashe kofin Firimiyar Ingila da Manchester City, sai dai a yanzu, Liverpool ta shiga gaban tawagarsa da tazarar maki 22 a teburin Firimiya, kuma saura wasanni 13 a karkare gasar.

Messi wanda sau shida ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya, ya kuma lashe kofin gasar La ligar Spain sau 10, yana da kwantiragi da Barcelona da sai shekarar 2021 zai kare.

Amma yanzu haka akwai takun saka tsakanin Messi da daraktan wasannin Barcelona Eric Abidal tun bayan da Abidal din ya zargi ‘yan wasan kungiyar da rashin sadaukar da kai a karkashin tsohon koci, Ernesto Valverde, lamarin da ya sa Messi ya nuna rashin jin dadinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.