Wasanni-Brazil

Tsananin cuta ya hana gwarzon dan kwallon duniya Pele zirga-zirga

Gwarzon dan wasa na duniya Pele dan Brazil da ya lashe kofin duniya sau 3 a tarihi.
Gwarzon dan wasa na duniya Pele dan Brazil da ya lashe kofin duniya sau 3 a tarihi. REUTERS/Christian Hartmann/File Photo

Rahotanni daga Brazil na nuna cewar tsohon tauraron kwallon kafar duniya Pele na fama da tsananin rashin lafiya, abinda ke hana shi barin gidan sa, saboda yadda baya iya tafiya da kafafuwan sa har sai an tura shi a keken guragu.

Talla

Dan tsohon tauraron kwallon kafar, Edinho ya ce mahaifinsa mai shekaru 79 na fama da matsalar motsa jikinsa, abinda ke sa shi yawan tunani da ke shafar lafiyar sa baki daya.

Edinho ya ce Pele na matukar jin kunyar fita bainar jama’a ana tura shi a keken guragu, la’akari da yadda ya yi rayuwar sa a matsayin Tauraro a fagen kwallon kafa, wanda ake girmamawa a kowacce kasa da ke duniya.

Har yanzu mutane da dama na kallon Pele a matsayin dan kwallon da ya fi kowa fice a fagen kwallon kafar duniya, kuma har ya zuwa yau shi ne dan wasa daya tilo da ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku a rayuwar sa, a shekarar 1958 da 1962 da kuma 1970.

Ya zuwa yanzu dai Pele ya takaita fita bainar jama’a tun bayan ziyarar da ya kai Paris a watan Afrilun bara, inda ya halarci wani biki tare da tauraron kwallon kafar Faransa Kylian Mbappe.

A shekarar 2014 an kwantar da shi a asibiti saboda matsalar cutar koda wadda ta shafi mafitsarar sa.

Rahotanni sun ce yanzu haka tsohon gwarzon dan wasa na da koda guda ne, bayan karya kashin hakarkarin sa wanda ya tilasta cire maas kodar.

Edinho ya ce mahaifin na sa na cikin yanayi mai kyau a yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.