Wasanni-Kwallon kafa

Guardiola na fargabar wasansu da Real Madrid a gasar zakarun Turai

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola. Reuters/Phil Noble Livepic

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce babban kalubalen da ke tunkaro shi yanzu haka a fagen tamaula bai wuce karawar tawagarsa da Real Madrid ta Spain karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai zagayen kungiyoyi 16 ba.

Talla

A zantawar Guardiola da jaridar wasanni ta Daily Football, ya ce babu shakka idan har Madrid ta yi waje da City daga zagayen na kungiyoyi 16 zai iya zama sanadin rasa aikinsa.

Manchester City mai rike da kambun Firimiya za a iya cewa ta faro wannan kaka da kafar hagu ganin yadda kambun ke neman subuce mata bayan da Liverpool ta dare saman Teburi tare da bata tazarar maki 22 bayan kaiwa rabin kaka.

Guardiola wanda yanzu haka ke cikin halin tsaka mai wuya ana ganin abu ne mai wuya City ta iya raba gari da shi ganin yadda ya shafe kakar wasa 2 a jere yana kai Club din ga nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila ko da dai ya gaza cikawa Club din burinsa na kai labari a gasar cin kofin zakarun Turai, kofin da bai taba zuwa gidan City a tarihi ba.

Ko a baya-bayan nan Guardiola ya bayyana zuwansa horar da Club karkashin gasar Firimiya a matsayin babban kuskure a rayuwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.