Wasanni

Ighalo yayi atasayen farko tare da takwarorinsa a United

Odion Ighalo na Najeriya da ya koma Manchester United da taka leda.
Odion Ighalo na Najeriya da ya koma Manchester United da taka leda. Getty Images

Tsohon dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo, yayi atasayen farko tare da sabbin takwarorinsa a Manchester United, bayan killace shi da kungiyar ta yi saboda annobar murar mashako ta Coronavirus.

Talla

A karshen watan Janairun da ya gabata, Mancester United ta kulla yarjejeniyar wucin gadi da Ighalo tsawon watanni shida daga kungiyarsa ta Shanghai Shenhua dake China, inda annobar murar ta bulla.

Sai dai bayan zuwan dan wasan United ta killace tsawon kwanaki 14 inda ya ci gaba da atasaye shi kadai, don kaucewa yiwuwar yaduwar murar ta Corona.

Ighalo na cikin tawagar ‘yan wasan Manchester United da a yau lahadi za su fafata da Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.