Wasanni

Lille ta sanya farashin fam miliyan 50 kan Osimhen

Kungiyar Lille dake Faransa ta sanya farashin Fam miliyan 50 kan dan wasanta na gaba Victor Osimhen ga duk kungiyar dake neman kulla yarjejeniya da shi bayan karewar kakar wasa ta bana.

Dan wasan gaba na Kungiyar Lille Victor Osimhen.
Dan wasan gaba na Kungiyar Lille Victor Osimhen. REUTERS/Susana Vera
Talla

Tun cikin shekarar bara manyan kungiyoyin kwallon kafa a Nahiyar Turai ke neman kulla yarjejeniya da Osimhen mai shekaru 20, kuma dan wasan gaba na tawagar Najeriya ta Super Eagles, biyo bayan kwarewar da ta bashi damar zama shiga sahun matasan ‘yan wasan nahiyar Turai dake kan gaba wajen jefa kwallaye a kakar wasa ta bana.

Daga cikin kungiyoyi masu neman dan wasan akwai, Barcelona, Real Madrid da kuma Liverpool.

A halin yanzu Osimhen ya ciwa kungiyarsa ta Lille dake gasar Ligue 1 kwallaye 14, gami da taimakawa wajen jefa wasu karin kwallayen 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI