Wasanni

Ba zan rabu da City saboda hukuncin UEFA ba - Guardiola

Mai horas da kungiyar Manchester City Pep Guardiola.
Mai horas da kungiyar Manchester City Pep Guardiola. REUTERS/Phil Noble

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce zai ci gaba da zama tare da kungiyar ko da kuwa ta yi rashin nasara a kotu, inda take neman soke hukuncin haramta mata shiga gasar cin kofin zakarun Turai tsawon shekaru 2.

Talla

Guardiola ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da hukumar gudanarwar Manchester City da kuma ‘yan wasan kungiyar, duk da fuskantar hukuncin haramcin shiga wasannin zakarun Turan guda 2 a nan gaba, da kuma rahotannin dake cewa kungiyar Juventus na kokarin tuntubarsa don kulla yarjejeniya da shi.

Yau talata ake sa ran kocin na City ya sanar da matsayar tasa ta ci gaba da kasancewa da kungiyar har zuwa karshen yarjejeniyarsa da ita a 2021 yayin taron manema labarai.

A makon jiya ne dai hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA ta yanke hukuncin na haramtawa Manchester City shiga gasar zakarun Turai tsawon shekaru 2, bayan samun ta da laifin kashe kudaden da suka wuce kima wajen sayen ‘yan wasa, sama da adadin wadanda take samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI