Wasanni-Kwallon kafa

Kwallon kafa za ta yi tinkaho da Mbappe - Ronaldo

Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG.
Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG. Reuters/Eric Gaillard

Cristiano Ronaldo ya yi amannar cewa dan wasan Paris Saint –Kylian Mbappe gwarzo ne kuma shi ne makomar wasan kwallon kafa.

Talla

Mbappe ya nuna jajircewa da hazaka, lamarin da ya sa ya kasance daya daga cikin shahararrun ‘yan wasa a duniya tun bayan da ya bayyana a kungiyar Monaco a shekarar 2016-17.

Tuni dai dan wasan mai shekaru 21 ya riga ya lashe kofin duniya, kofin gasar Ligue 1 na Faransa 3 da wasu kofuna 3 a Faransa da ya ci wa kungiyarsa PSG da Monaco.

Ronaldo wanda sau 5 ya ke lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ya jinjina wa Mbappe, wanda ake ta alakanta shi da komawa Madrid ko Juventus, inda ya ke cewa dan wasa ne da zai kawata kwallon kafa ko a nan gaba.

Dan wasan da a ake sa ran zai gaji Ronaldo da Messi wajen gwada bajinta a wasan kwallon kafa, ya ba ‘mara da kunya’ a kungiyar PSG da ke babban birnin kasar Faransa.

Bayan ya ci kwallaye 39 a dukkanin gasanni a kakar da ta gabata, a halin da ake ciki, Mbappe na da kwallaye 24, kuma 15 daga cikinsu a gasar Ligue 1 ya ci su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.