FIFA

FIFA tace ana iya soke wasanni saboda barazanar coronavirus

Shugaban FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino. Attila KISBENEDEK / AFP

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino yace barazanar kamuwa da cutar coronavirus na iya tilasta soke wasannin kasa da kasa da aka shirya.Infantino yace rayuwar jama’a ya fi duk wata harkar kwallon kafa, saboda haka babu dalilin cigaba da gudanar da wasannin a yankunan da ake fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Talla

Shugaban Hukumar yace idan hali yayi ana iya dakatar da wasannin ko kuma gudanar da su ba tare da Yan kallo ba domin kare lafiyar jama’a.

A kasar Italia an soke wasanni guda 5 da aka shirya gudanarwa a karshen wannan mako saboda yadda cutar ke yaduwa a kasar cikin su harda karawa tsakanin Juventus da Inter Milan.

A kasar Switzerland ma an soke wasannin sakamakon umurnin da gwamnati ta bayar na hana taron jama’ar da suka wuce 5,000.

Ita ma gwamnatin Faransa ta sanar da soke gudun yada kanin wani da aka shirya gobe lahadi saboda barazanar cutar, yayin da aka dakatar da tseren Formula One a China da wasannin tseren da aka shirya a Shanghai da kuma gasar zari ruga a Ireland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.