Wasanni-Kwallon kafa

Wannan rashin nasarar za ta amfane mu - Klopp

Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila.
Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila. REUTERS/Charles Platiau

kocin Liverpool Jurgen Klopp bai bari abin ya mai ciwo ba, duk da dukan kawo wuka da tawagarsa ta sha a hannun Watford, a wasan da ta yi rashin nasara karon farko a cikin wasan gasar firimiya 44 da ta buga, inda ya ce yanzu babu sauran matsin lamba.

Talla

Kocin ya ce kafin wannan rashin nasarar, ‘yan wasansa, da shi kansa na cikin matsin lambar ganin cewa kungiyar ta kammala wannan kaka ba tare da an yi galaba a kansu ba.

Liverpool dai ta ziyarci gidan Watford Vicarage Road road ne da bajintar cin wasanni 18 a jere, kuma saura ta lashe guda ta kafa sabon tarihi, yayin da kuma ta ke wasanni 44 ba tare da an doke ta ba.

Amma Watford ta buga wasa mai armashi don baiwa Liverpool mamaki, har ya kai ga taka mata birki, inda Ismaila Sarr ya ci kwallaye biyu, ya kuma taimaka Troy Deeney ya saka daya a raga; wasa ya tashi Watford na da 3 Liverpool 0.

Wannan rashin nasara dai ba zai bata tafiyar Liverpool na lashe gasar Firimiyar Ingila ba saboda tazarar maki 22 ta bada a gasar, amma ya taka mata birki a kokarin da take na zama kungiya ta biyu da ta yi wasa ba tare da shan kashi ba a kaka guda a tarihin gasar.

Sai dai Klopp yana gani wannan al’amari ne mai amfani idan aka dube shi a mahanga ta ‘matsin lamba’, duba da cewa yanzu ‘yan wasansa za su yi wasa ne hankali kwance.

Kocin na Liverpool ya ce, “da ma dole ne mu yi rashin nasara, kuma ga ranar ta zo”

Kamar yadda aka zata, kocin Watford Nigel Pearson ya yi matukar mamakin ganin yadda kungiyarsa ta lalasa Liverpool, sai dai yana daukin ganin ya tabbatar da cewa ba nasarar banza ce ya samu ba, saboda yanzu haka kungiyar na jerin wadanda akwai yiwuwar su rikito daga gasar Firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.