Wasanni-Olympics-coronavirus

Mai yiwuwa a dage gasar Tokyo 2020 saboda cutar Coronavirus

Ministar wasannin Olympics na kasar Japan ta ce mai yiwuwa a dage gasar ta Tokyo 2020 har zuwa wani lokaci a wannan shekarar, sakamakon fargabar cutar coronavirus.

Kwamitin shirya gasar Olympics ta tabbatar da cewa gasarTokyo 2020 na nan daram.
Kwamitin shirya gasar Olympics ta tabbatar da cewa gasarTokyo 2020 na nan daram. REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Yayin da take amsa tambayoyi a majalisar dokokin kasar, Seiko Hashimoto ta ce yarjejniyar kasar da kwamitin shirya gasar Olympic ita ce a yi gasar a cikin shekarar 2020.

Ana iya fassara haka da cewa ana iya dagewa ko jinkirta gasar da aka shirya cewa za ta gudana a ranar 24 ga watan Yuli zuwa 9 ga watan Agustan wannan shekarar.

Cikin yarjejeniyar daukan nauyin wannan gasa, kwamitin shirya gasar na duniya ne ke da hurumin soke gasar.

A halin da ake ciki har an dage, ko kuma soke wasu gasannin motsa jiki masu mahimmanci sakamakon bullar wannan cuta ta coronavirus, ciki har da gasar tseren motoci ta Chinese Grand Prix da aka shirya yi a birning Shangahai na China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI