Wasanni

Coronavirus ta hana karawa tsakanin Juventus da AC Milan

An dage wasa tsakanin Juventus da AC Milan zagaye na biyu a gasar Italian Cup a birnin Turin saboda fargabar cutar Coronavirus wadda ta yi mummunar barna cikin sa'o'i 24 a Italiya.

Coronavirus ta hana gudanar da zagaye na biyu tsakanin Juventus da AC Milan a gasar Italian Cup
Coronavirus ta hana gudanar da zagaye na biyu tsakanin Juventus da AC Milan a gasar Italian Cup Yahoosports
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Kare Fararen Hula ta Italiya ta ce, mutane 27 sun gamu da ajalinsu cikin sa’o’i 24 a sanadiyar annubar, abin da ya sa adadin mutanen da cutar ta lakume ya kai 79 a kasar.

Tuni aka haramta gudanar da harkokin wasanni a wasu yankuna uku na Italiya da suka hada da Lombardy da Veneto da Emilia Romagna.

Nan gaba ne za a sanar da ranar da za a kece rainin tsakanin Juventus da AC Milan a kwanton wasansu.

Da ma a yau Laraba ne aka shirya karawar tsakanin kungiyoyin biyu a Allianz Arena bayan sun tashi kunnen doki 1-1 a karawarsu ta zagayen farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI