Wasanni

Mun tafka manyan kurakurai a wasanmu da Chelsea- Kloop

A karo na uku kenan da Liverpool ke shan kashi a wasanni hudu da ta buga
A karo na uku kenan da Liverpool ke shan kashi a wasanni hudu da ta buga REUTERS/David Klein

Chelsea ta yi waje da Liverpool a gasar FA bayan ta doke ta da ci 2-0  a Stamford Bridge, abin da ya bai wa Chelsea damar tsallakawa matakin wasan dab da na kusan karshe, wato Kwata-Fainal.

Talla

Williams da Ross Barley ne suka ci wa Chelsea kwallayen biyu, yayin da kocin Liverpool, Jurgen Kloop ke cewa, har yanzu kaka mafi kayatarwa ga kungiyar ba ta zo ba tukunna.

Kloop ya yi sauye-sauye har guda bakwai a cikin tawagar da ta buga masa wasan da Watford ta doke ta a ranar Asabar, wanda a karon farko kenan da kungiyar ke shan kashi cikin wasanni 45 da ta buga a gasar firimiyar Ingila.

Kocin ya bayyana cewa, kashin da suka sha a hannun Chelsea, ba abu ba ne mai kyau, yana mai cewa, sun tafka manyan kurakurai guda biyu wajen jefa kwallaye a raga.

Kodayake a bangaren gasar firimiyar Ingila, har yanzu Liverpool na jiyo kamshin lashe kofin na firimiya a karon farko cikin shekaru 30, lura da cewa ta bayar da tazarar maki 22 a teburi.

Liverpool na bukatar samun nasara a wasanni hudu kafin lashe kofin firmiya a bana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.