Wasanni

An dage wasannin Seria A a Italiya saboda annobar Coronavirus

Coronavirus na kawo rudani a a bangaren wasannin Italiya, inda aka daga wasanni
Coronavirus na kawo rudani a a bangaren wasannin Italiya, inda aka daga wasanni Emilio Andreoli/Pool via Reuters

A kasar Italiya, za a yi dukkannin wasanin motsa jiki ba tare da ‘yan kalo a filin wasa ba, a kokarin da gwamnatin kasar ke yi na yaki da cutar Coronavirus ko kuma COVID 19.

Talla

Wasannin sun hada da na mata da maza da illahirin wasannin gasar kasar Italiya ta Serie A, kuma za a ci gaba a hakan ne har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu mai zuwa.

Italiya ce kasar da wannan cuta ta fi muni, inda yanzu haka sama da mutane dubu 3 suka harbu da ita, sannan ta aika da 107 lahira.

A wananna makon ma, an dage wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kalubalen Italiya da za a yi tsakanin Juventus da Inter Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.