Wasanni-Brazil

An kama Ronaldinho a Paraguay

An kama tsohon shahararrern dan wasan kasar Brazil Ronaldinho a Paraguay, sakamakon zarginsa da ake da amfani da takardun bogi wajen shiga kasar.

Tsohon Dan wasan Brazil Ronaldinho
Tsohon Dan wasan Brazil Ronaldinho sportskeeda.com
Talla

Hukumomin Paraguay din sun ce an tsare dan shekara 39, wanda a shekarar 2002 ya lashe kofin duniya da kasarsa Brazil da shi da dan uwansa Roberto a wani otel dake wani lambun wasan kwallon golf a daren Laraba.

Rahotanni sun ce an samu fasfo 2 masu dauke da sunan Ronaldinho da dan uwansa Roberto da ke nuna cewa su ‘yan kasar Paraguay ne a dakin otel din da suka kama

Har yanzu dai ‘yan uwan biyu za su ci gaba da kasancewa a tsare har sai hukumomin kasar sun bayar da sanarwa a wannan safiya ta Alhamis.

Wata sanarwa daga hukumar ‘yan sandan Paraguay ta ce Ronaldinho da tawagarsa sun shigo kasar ne bisa gayyatar wani mai gidan caca na, casino Nelson Belotti.

An sa ran tsohon dan wasan kasar Brazil din, wanda ya buga wa Barcelona wasa har ya kai ga lashe kofin zakarun nahiyar Turai za halarci wasu jerin bukuwa a Paraguay, inda aka gayyaci kafafen yada labarai su kasance don shaida ganawarsa da masoyansa da wasu manayan mutane.

Yanzu haka dai Ronaldinho ba shi da fasfo din kasarsa Brazil, sakamakon tarar da aka mai daga hukumar kare muhallin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI