Kofin FA: Man City zata kara da Newcastle, Arsenal da Sheffield
Manchester City dake rike da kofin kalubalen Ingila za ta yi tattaki zuwa Saint James Park don fafatawa da Newcastle a matakin daf da na kusa da karshe wato quarter finals.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Arsenal, wacce ta kafa tarihin lashe kofin sau 13, za ta ziyarci Sheffield United, yayin da Chelsea, wacce rabonta da lashe kofin tun shekarar 2018, za ta tafi filin King power don gwada kwanji da Leicester City.
Norwich za ta karbi bakunci Manchester United ko kuma Derby, wadanda a yau Alhamis za su yi wasansu.
A tsakanin ranakun karshen mako, na ranar 21 da 22 ga watan Maris za a yi wasannin.
Tawagar Pep Guardiola ta Manchester City ta kai wannan mataki ne bayan doke Sheffield Wednesday da ci daya mai ban haushi, a hobbasar da take na ci gaba da tasiri a cikin gida da ma nahiyar.
Arsenal ta kasance ta farko cikin wadanda suka tsallake, bayan nasarar da ta yi kan Portsmouth a ranar Litinin, yayin da Sheffield United ta samu tsallakawa wannan mataki a karon farko tun shekarar 2014.
A ranar Talata, Chelsea ta doke Liverpol mai jan ragamar gasar Firimiya 2-0, kwallayen da Willian da Ross Barkley suka ci, yayin da Leicester City ta yi galaba kan Birmingham da ci daya mai ban haushi, kwallon da Ricardo Pereira ya ci a kusan karshen wasa.
Norwich ta kai wannan matakin daf da na kusa da karshe ne a karon farko tun kakar 1991-92 ta wajen nasara kan Tottenham 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan sun yi kunnen doki 1-1.
Ga yadda jadawalin matakin daf da na kusa d karshe na kofin FA yake:
Sheffield United da Arsenal
Newcastle da Manchester City
Norwich da Derby/Manchester United
Leicester City da Chelsea
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu