Wasanni

Manchester United ba tsarar Manchester City ba ce

'Yan wasan Manchester United sun kewaye Raheem Sterling na Manchester City a Old Trafford
'Yan wasan Manchester United sun kewaye Raheem Sterling na Manchester City a Old Trafford Reuters

A karon farko ckin shekaru 10 Manchester United ta doke Manchester City a jere da juna, yayin da kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya yi amanna cewa, dangon alaka tsakanin ‘yan wasansa da magoya bayan kungiyar na dawowa a yanzu.

Talla

Kalaman kocin na zuwa ne bayan nasarar da suka samu karo na biyu a jere akan abokiyar hamayyarsu Manchester City a Old Trafford a gasar firimiyar Ingila.

Solksjaer ya ce, karawar hamayya suka yi da Manchester City kuma ‘yan wasansa da magoya baya duk sun nuna shaukinsu.

Manchester United ta dare matsayi na biyar a teburin firimiyar Ingilar, abin da ka iya ba ta damar samun gurbi a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta kaka mai zuwa musamman muddin Manchester City ta gaza samun nasara a karar da ta daukaka na kalubalantar matakin haramta mata buga Gasar Zakarun Turai har tsawon kaka biyu.

A bangare guda, kocin Manchester City Pep Guardiola ya hakikance cewa, ‘yan wasansa sun taka leda yadda ya kamata, amma dan wasansa na tsakiya, Bernando Silva ya ce, rawar da suka taka ba mai kayatarwa ba ce.

Sau bakwai kenan Manhester City ke shan kashi a gasar firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.