Wasanni

Zamu sayar da Aguero idan muka sha kaye a Kotu - City

Sergio Aguero dan wasan gaba na Manchester City.
Sergio Aguero dan wasan gaba na Manchester City. Reuters/Carl Recine

Kungiyar Manchester City tace a shirye take ta sayarda dan wasanta na gaba Sergio Aguero idan har hukuncin haramta masa shiga gasar cin kofin zakarun turai na tsawon shekaru 2 ya tabbata.

Talla

Yanzu haka dai City ta garzaya kotun sauraron kararrakin wasanni ta duniya domin neman soke hukuncin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta kakaba mata na haramcin shiga gasar Zakarun Turan.

FIFA ta yanke hukuncin kan City ne bayan samun kungiyar da laifin kashe makudan kudade wajen sayen ‘yan wasa da suka zarta adadin wadanda take samu a matsayin riba, laifin da kungiyar ta Manchester City ta musanta aikatawa.

A baya bayan nan ne kuma City ta ce idan suka yi rashin nasara a kotun kararrakin wasannin a shirye take ta baiwa dan wasanta Aguero damar komawa wata kungiyar domin haskawa a gasar Zakarun Turai.

Yanzu haka dai kakar wasa 1 da rabi ta ragewa Sergio Aguero kammala yarjejeniyar da ya kulla da City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI